Saturday, March 9, 2024

Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi a Nijeriya ta ce a fara duban jinjirin watan Ramadana daga ranar talaka....











Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi a Nijeriya ta ce a fara duban jinjirin watan Ramadana daga ranar talaka....

Kwamitin duban wata na Najeriya ya umarci ƴan kasar da su fara duban jaririn watan azumin Ramadan daga ranar Lahadi.

Wata sanarwa da kwamtin ya fitar, ta ce Lahadi ce 29 ga watan Sha’aban, rana kuma ta farko da za a duban watan na azumi.

Don haka ne, Kwamitin duban watan (NMSC), ya umarci duk wanda ya ga jaririn watan na azumi da ya yi kokarin sanar da ita ta hanyoyi da aka saba.

A ranar Litinin ne, ake sa ran al’ummar Musulmi a faɗin duniya za su tashi da azumi idan har aka ga wata a gobe Lahadi.

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home