Saturday, March 9, 2024

Da ace maza zasu koma haihuwa sai mijina ya haifi ƴaƴa 20 zan barshi ya huta—Mariya











Da ace maza zasu koma haihuwa sai mijina ya haifi ƴaƴa 20 zan barshi ya huta—Mariya

Kamar dai yadda kuka sani ƴan mata da samari na baje kolinsu a shafukan sada zumunta na zamani wato Social Media.

Inda wasu ke amfani da kafafen na sada zumunta irin su Facebook, Twitter, Instagram, da dai sauransu wajen gudanar da harakokin da suka shafi kasuwanci.

Wasu kuma ke yin rubuce-rubuce da nufin jan hankalin mabiyansu wato followers, ta yadda za kuga ƴan mata da samari na yin abubuwan da zasu ɗauki hankulan abokansu na sada zumunta.

Wata matashiya da ke zama ɗaya daga cikin masu amfani da shafin Twitter ta yi wani rubutu wanda ya ɗauki hankalin mabiyanta kamar haka, “Misali ace maza su kona haihuwa, nawa kike so mijinki ya haifa miki? yasin sai ya haifa min ƴaƴa 20 sannan zan bar shi ya huta” in ji ta.

Kamar yadda za ku gani a hotonki Screenshot ɗin rubutunta da muka ɗauko muku gashi nan daga ƙasa.

Mariya tace da ace maza zasu dawo haihuwa sai mijinta ya haifa mata ƴaƴa 20 sannan zata bar shi ya huta

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home