Friday, March 8, 2024

An naɗa Sheikh Yasir Ad Dawsary a matsayin babban limamin Haramin Makkah











An sake naɗa Sheikh Yasir Ad Dawsary a matsayin babban limamin Masallacin Harami na Makkah.

Sheikh Dawsary, wanda aka naɗa shi bisa umarnin Shugaban Babban Ofishin Kula da Masallatan Harami guda Biyu, Sheikh Abdul Rahman As Sudais, zai kwashe shekaru 4 a kan muƙamin.

Hakazalika, ofishin ya kuma naɗa Sheikh Ahmad Al Hudaify da Sheikh Khalid Al Muhanna a matsayin manyan limaman Masallacin Ma’aiki Sallallahu alaihi Wasallama a Madina, su ma na tsawon shekara 4.

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home