Saturday, March 9, 2024

Wata mata ta biyawa kishiyarta aikin Hajji a jihar Nassarawa











Wata mata ta biyawa kishiyarta aikin Hajji a jihar Nassarawa


Labarin matar data biyawa kishiyarta kujerar aikin Hajji da kuɗin ajiye aikinta ya ja hankalin mutane a ciki da wajen jihar, Nasarawa inda dubban jama'a suke ta yi mata fatan alheri da gamawa lafiya, matar tace wallahi zaman lafiyar da suka shafe shekaru suna yi da juna ne yasa ta biya mata Makka ba'a taɓa jin kansu ba kowa na zaune da kowa da zuciya ɗaya

Ita ma wacce aka biya mawa tace wallahi abin ya bata mamaki kuma dama ta faɗa mata cewa da zarar an biyata kuɗin ajiye aiki zata biya mata aikin Hajji sai gashi ta cika alƙawari, muna fatan Allah ya saka mata da Alheri ya bamu mata nagari

Kunji fa menene ra'ayoyinku shin kuna ganin za'a iya samun macce kishiya irin wannan a garinku?

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home