Masu garkuwa da mutane da macizai su ka riƙa yi mana azaba — Waɗanda aka sace
Wasu mutane da aka yi garkuwa da su kwanan nan daga hannun wadanda aka yi garkuwa da su sun bayyana cewa masu garkuwa da mutane sun azabtar da su da macizai masu dafi.
Wasu daga cikinsu wadanda suka bayyana irin halin da suka shiga a hirarsu da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, sun ce akwai macizai da dama a cikin dazuzzukan da ‘yan fashin ke zaune a Kaduna, da Kala-Balge da ke kusa da tafkin Chadi a Borno.
Sauran yankunan sun hada da Shaki a Jihar Oyo, Borgu da Kagara a Nijar, Karim Lamido a Adamawa, da Lau a Taraba.
Sun ce macizan na saran masu garkuwa da mutanen da kuma wadanda aka yi garkuwar da su.
Daya daga cikinsu, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya shaida wa NAN cewa masu garkuwa da mutane na jefa su a wuraren da macizai suka mamaye.
“Masu garkuwan sun san wuraren da macizan suka mamaye kuma sai su jefa mu a wurin.
“Da mutum ya ga macizai, sai tsoro ya kama su kuma za su so su gudu. To suna tsorata mutane da macizan ne don su kawo kudin fansa.
“Shi ne fa sai kaga wadanda aka yi garkuwa da su na fadawa yan uwa da abokai da su sayar da komai na su – gida, filaye, motoci, kayan gida, takalma, komai kawai – don tara kudin fansa.”
“Da dare ya fi tayar da hankali. An bar ku a waje, cikin duhu, sai dai ku ji maciji kan kafafunku.
“Lokacin da nake hannun su, macizai sun sari wasu daga cikin mu da dama. Su ma masu garkuwa da mutanen ba su tsira ba domin wasun su ma sun cije su,” wani da aka kai wani dajin da ke Kagara a Nijar ya shaida wa NAN.
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home