Thursday, February 22, 2024

Dangote, BUA da sauransu sun amince da rage farashin siminti a Nijeriya











Masu kamfanin sarrafa siminti a Najeriya sun amince su rage farashinsa zuwa tsakanin naira dubu bakwai da naira dubu takwas kan buhu mai nauyin kilogram 50.

Masu kamfanin sarrafa siminitin sun bayyana cewa a shirye suke su rage farashin nan gaba da zarar gwamnatin tarayya ta cika alƙawurranta.

Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa an cimma wannan matsaya ne tsakanin gwamnati da masu kamfanin a wani taro da ministan ayyuka, Sanata David Umahi ya kira ranar Litinin a Abuja, babban birnin ƙasar.

Kamfanonin Dangote da BUA da Lafarge Africa sun amince cewa farashin siminti ba zai wuce tsakanin naira dubu bakwai da naira dubu takwas kan kowane buhu mai nauyin kilogram 50 – ya danganta da yankin.

Taron ya samu halartar ministar harkokin masana’antu da kasuwanci da hannun jari, Doris Uzoka-Anite.

Doris Uzoka-Anite ta ce ana ƙoƙari wajen magance matsalolin da suka haifar da ɗagawar farashin simintin baka-tatan.

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home