Thursday, February 22, 2024

Kotu ta aike da ƴar TikTok gidan yari bisa iƙrarin yin maɗigo











Wata kotun shari’a a jihar Kano ta tura wata ƴar Tiktok, Ramlat Princes zuwa gidan gyaran hali bayan hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama ta da zargin baiyana cewa ita ƴar madigo ce a wani faifan bidiyo.

Jami’an hukumar Hisbah ne dai su ka kama Ramlat a ranar Alhamis, kwanaki bayan wani faifan bidiyon ta ya nuna tana shelanta madigo.

An tattaro cewa an kama ƴar Tiktok din ne bayan faifan bidiyonnya jawo alla-wadai tsakanin masu amfani da shafukan sada zumunta, wadanda suka yi kira da a kama ta.

Hukumar Hisbah ta gurfanar da Ramlat a gaban Kotun Shari’ar Musulunci, inda aka tuhume ta da laifin yada baɗala a shafukan sada zumunta da kuma tunzura jama’a.

Alkalin Kotun ta Shari’ar Musulunci, Sani Tanimu Hausawa ya bayar da umurnin a ci gaba da tsare wacce ake zargin, wacce aka ce ta amsa laifin ta.

Alkalin kotun ya ba da umarnin a ci gaba da tsare Ramlat har zuwa ranar Litinin 19 ga Fabrairu, 2024 lokacin da ake sa ran za a yanke mata hukunci.

Ramlat, ƴar kasar Ghana, wacce ke a jihar Taraba, ta shaidawa jami’an Hisbah cewa ta zo jihar Kano ne domin ta ziyarci yar uwar ta da ke zaune a unguwar Gaida a cikin birnin Kano, kimanin wata daya da ya gabata.

A cikin sakon da ta wallafa, an nuna Ramlat din na cewa duk mutumin da yake son aurenta dole ne ya amince ta auri “matar ta” kafin ta amince da auren.

“Duk mutumin da yake so ya aure ni ya sani dole ne in auri matata in ba haka ba, ba zan yarda da shi ba.

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home