Kotu ta bada umarnin a duba ƙwaƙwalwar Murja tare da ɗage zaman shari’ar zuwa watan Mayu
A yau Talata ne wata kotun shari’ar Musulunci a jihar Kano ta bayar da umarnin a kai shararriyar ƴar TikTok din nan mai suna Murja Kunya zuwa asibitin gwamnati domin a duba lafiyar ƙwaƙwalwar ta.
Murja,wacce ke zaune a unguwar Tishama Hotoro a Kano, na fuskantar shari’a kan tuhume-tuhume guda uku da suka hada da tada hankalin jama’a, alaƙa da gungun masu aikata laifuka da kuma tsoratarwa.
Da ya ke yanke ƙwarya-ƙwaryan hukunci, Alkalin kotun, Nura Yusuf Ahmad, ya bayar da umarnin a kai wacce ake kara asibitin gwamnati domin a tabbatar da lafiyar ƙwaƙwalwar ta saboda zargin da ake yi mata na shan miyagun kwayoyi.
“Bayyanar ta a baya ta nuna cewa ba ta cikin hayyacinta saboda zargin tasirin miyagun kwayoyi.
“Hukumar Hisbah za ta riƙa samar da kotu akan lafiyar wacce ake kara lokaci zuwa lokaci har tsawon wata uku.”
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home