Tuesday, January 16, 2024

VIDEO: “Ya halatta macce ta yarda ayi Zina da ita don a bata abinci taci”—Maqari











VIDEO: “Ya halatta macce ta yarda ayi Zina da ita don a bata abinci taci”—Maqari


Fitaccen Malamin Islamar nan na Duniya Sheikh Ibrahim Maqari ya bada fatawar cewa ya halatta macce ta bada jikinta ayi Zina da ita don a bata abinci taci bisa lalura, malamin yace "Ba ina faɗin wannan magar ne a babin talauci ba a'a ba zai yiwu don talauci da rashin babu ace macce tayi Zina, saboda Allah SWT cewa yayi kar mu kusanceta ma ballantana mu aikata, amma ita lalura tana shafe duk wani hukunci komai girmansa a addinin Musulunci, 

Saboda haka idan macce ta shiga halin ƙaƙa nikayi ta rasa inda zata sa kanta tayi nema bata samu ba, tayi bara bata samu ba ta nema an hana ta, kuma zata iya mutuwa idan bata ci abincin ba, sannan aka nemi dole sai ta bada kanta anyi Zina da ita don a bata abincin to babu laifi ya halatta ta yarda don a bata abincin taci ta rayu," In ji shi kamar yadda ya bayyana cikin Bidiyon nan ku kalla ku bayyana mana ra'ayoyinku

Menene ra'ayoyinku shin kun gamsu da wannan fatawa ta shehin malamin?

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home