Munfara shirin daukar matakin doka kan masu raye raye a soshiyal midiya – Abba El-Mustapha
Munfara shirin daukar matakin doka kan masu raye raye a soshiyal midiya – Abba El-Mustapha
Hukumar tace fina-finai da dab’i ta jihar Kano, ta magantu kan korafin da al’umma ke yi dangane da yadda wasu ke amfani da shafukan sada zumunta, musamman ma Tiktok da Facebook, da Youtube wajen yin abubuwan da basu dace ba
Ta cikin shirin Zauren Premier, shugaban hukumar tace fina-finai da dab’i ta jihar Kano, Abba El-Mustapha, ya ce nan gaba kadan hukumar za ta bullo da wata hanyar daukar matakin kan masu raye-raye da shirya bidiyon da ya sabawa al’ada da addini.
Sai dai bai yi karin bayanin kan ko hakan na nufin gyara a dokar da ta kafa hukumar ba.
“Wannan zai zama a straight warning, da duk wanda yake abusing social media musamman Tiktok, Tiktok duk wani dan jihar Kano ya kwana da shirin cewar mun kusa zuwa gunsa”
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home