Za a fara tace ɗanyen mai cikin Disamba, a Matatar Fatakwal - Ƙaramin Ministan Fetur...
Gwamnatin Najeriya ta ce Matatar Fetur ta Fatakwal za ta fara tace ɗanyen mai a cikin watan Disamba.
Cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran NNPC, Garba Deen Muhammad ya fitar a ranar Juma’a, ya ce matatar za ta koma aiki nan da wata huɗu, ƙarshen shekara kenan.
Matatar Ɗanyen Mai ta Fatakwal dai na da ƙarfin iya tace ganga 60,000 ce a kowace rana. An kulle ta a cikin 2019, domin gyara, bayan gwamnati ta samu haɗin guiwar yarjejeniya da kamfanin Maire Texnimont ma Italy, wanda aka bai wa kwangilar gyaran matatar.
An bai wa kamfanin mai Eni kwangilar aikin bada shawarwarin gyare-gyare ga kamfanin da ke gyaran matatar.
Cikin 2021 NNPCL ya ce an fara gyaran bayan Majalisar Zartaswa ta amince da biyan dala biliyan 1.5 kuɗin gyara.
Sai dai kuma ko a cikin 2021, sai da Ƙaramin Ministan Fetur na lokacin, Timipre Sylva, ya ce matatar za ta fara aiki a cikin Disamba, 2022. Sai dai hakan bai yiwu ba.
Sannan cikin watan Janairu, 2023, Sylva ya ce matatar Fatakwal za ta fara aiki zuwa Afrilu, 2023. Nan ma ɗin dai alƙawarin ba a cika shi ba.
Sai dai kuma sanarwar da Muhammad ya fitar a ranar Juma’a ta sake alƙawarin ne bayan Ƙaramin Ministan Fetur Heineken Lokpobiri da Shugaban NNPCL Mele Kyari sun kai ziyarar gani-da-idon yadda aikin gyaran Matatar Fatakwal ɗin ke tafiya.
Lokpobiri ya ƙara da cewa ya gamsu dangane da yadda aikin gyaran Matatar Fatakwal ɗin ke gudana. “Da zaran an kammala aikin har aka fara tace ɗanyen fetur a gida, sannan aka gyara sauran matatun fetur, to za a yi bankwana da matsalar fetur. “Sannan kuma tattalin arziki zai ƙaru, saboda za a daina fitar da Dala waje don a sayo tataccen fetur daga ƙasashen waje.”
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home