An umarci sojojin Nijar su yi shirin ko-ta-kwana
Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun bukaci dakarunsu da su yi shirin ko-ta-kwana, inda suka ce akwai karin barazanar kai musu hari.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa wannan gargadin yana kunshe a cikin wata takarda wadda shugaban sojin Nijar ya saka wa hannu.
Takardar, wadda aka watsa sosai a kafafen sada zumunta a ranar Asabar, ta bayyana cewa wannan umarnin da aka bayar kan cewa sojojin su kasance cikin shirin ko-ta-kwana zai sa su mayar da martani kan kowane irin hari da za a iya kai musu.
Labari mai alaka:
Dangantaka na kara tsami tsakanin Nijar da wasu kasashen duniya da kuma kungiyar ECOWAS duk da a ‘yan kwanakin nan alamu sun nuna ana samun ci gaba a yunkurin yin sulhu.
A makon nan sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sun bai wa jakadan Faransa kwana biyu ya fita daga kasar.
Haka kuma a kwanakin baya sojojin na Nijar sun tabbatar da cewa za su iya yin komai amma ba za su mayar da Shugaba Bazoum kan mulki ba kamar yadda ECOWAS ta bukata cikin gaggawa.
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home