Sunday, August 6, 2023

da Tirelar Dangote, Ya Ɓurma Gida Ya Murƙushe Yara 3











Abdul ya ce sun yi nasarar zama da direban, ya sa hannu a takarda domin bincike. Wani malamin addini a Unguwar Juma ya zanta da Legit.ng Hausa a jiya, ya kuma tabbatar da cewa abin ya faru ne yayin da ake barci. Abin da ya faru a ranar Ibrahim Zubairu wanda mazaunin unguwar ne ya ce bayan abin ya faru, mahaifin yaran ya fada masu su je su kwanta ganin akwai hadari a gari. Farkwarsa ke da wuya, sai kurum ya tsinci kan shi a gadon asibiti. Sai bayan an sallamo shi ya fahimci cewa ‘ya ‘yansu uku sun rasu cikin daren. Al-Mustapha, ‘dan autan Malam Abdu Zailani ne kadai wanda ya tsira domin yana tare da mahaifiyarsa. Mahaifiyar yaran ta ce ta na iya tuna lokacin da ‘ya ‘yanta su ka tafi daki domin su kwanta, ita kuma ta rufe masu kofa sai ta wuce makwancinta a gidan. Abin da ta ji bayan nan shi gini ya fado mata, sai ta ji Bayin Allah su na kokarin ceto su bayan motar ta auko masu, a haka aka iya kawo masu karen-mota-ya-yi-karambani-da-tirelar-dangote-ya-auka-gidan-ya-murkushe-yara/

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home