Friday, July 21, 2023

Uwa Ta Fashe Da Kuka Da Ganin Yadda Wanzami Yake Cirewa Dan Ta ‘Yarwuya, Uvulectomy....







Al’adar Cire ‘Yar Wuyan Jarirai A Turancin Likita ” Traditional Uvulectomy ” Dadaddiyace A Kasar Hausawa. Masana Kiwon Lafiya Sun Tabbatar Da Cewa Abin Da Bahaushe Ke Cewa ‘Yaruwa, Me Kama Da Tsiro A Cikin Baki Daga Sama.


Rumbune Dake Dauke Da Kwayoyin Garkuwar Jiki Dan Yakar Cututtuka Da Dama. Sedai, Al’adar Cire ‘Yar wuyan Jarirai Da Da Dade Musamman A Kasashen Hausawa Da Wasu Kasashen Afrika.


Hasawa Sunce Tsirone Wanda Da Yakan Iya Cutar Da Jariri Lokacin Shayarwa Da Ciwon Makogaro Bayan Ya Girma. Wannan Al’adar Ta Sa6a Da Binciken Kiwon Lafiya.


Suncce Cire ‘Yarwuya Yana Jefa Lafiyar Jaririn Cikin Hatsari Kamar:


1)- Yiwa Jaririn Mummunan Ciwo Miki/Tabo A Ganɗa.

2)- Ciwon Ganɗa Da Kubirinta.

3)- Ballewar Jini, Musamman Ga Jariran Da Aka Haifa Da Larurar Tsinkewar Jini Bayan Ciwo.

4)- Shigar Da Kwayoyin Cututtuka Ta Hanyar Askar Da Akai Amfani Da Ita Dan Cire ‘Yarwuyan.


5)- Shigar Da Kwayar Cuta Me Janyo Kamewar Da Kakkafewar Jiki “Tetanus” Saboda Yi Da Aska Me Tsatsa.


6)- Matsalar Shayarwa Saboda Raunata Hanka, Jariri Kan Fuskanci Wahalar Hadiyar Nono Yayin Shayarwa.


 

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home