Saturday, July 22, 2023

Shekara 7 Na Yi Ina Rubuta Waƙar Da Na Yiwa Manzon Allah — Alan Waƙa











Shaharran mawakinnan Hausar nan, Aminuddeen Ladan Abubakar ‘, wanda aka fi sani da Alan Waƙa, ya ce ya dauki kimanin shekaru 7 ya na rubuta waƙar da ya yiwa fiyayyen halitta, Manzon Allah (S.AW), wacce ya sanyawa suna “Muhammadu miftahul futuhati linzamin rayuwata”.


Hakazalika yace ita waka “Mufitahul futuhati” littafi ne ya mayar da shi waka saboda mutane da dama su amfana, inda ya ƙara da cewa babu shakka mutane sun ji dadin wakar “kuma nima Ina alfahari da ita.”

Ya ce mafiyawan wakokinsa yana gina sune kan Ilimi kuma yana gudanar da bincike kafin yayi kowacce irin waka, inda ya ce “domin yin hakan shi yake bani damar fadin abun da yake dai-dai akan duk wanda zai yiwa waka.


KALLI VIDEO 👇



0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home