Saturday, July 8, 2023

Saurayi ya cinnawa Gidan su budurwar sa Wuta bayan an Daura aurenta da wani buzu......











Wakilin sashin Hausa ya ce yanzu haka ƴan unguwar na can suna ƙoƙarin kashe wannan Wuta da saurayin ya cinnawa gidan su budurwar tasa saboda an ɗaura aurenta da wani ma'aikacin kamfanin mai na ƙasa NNPC a ɗazu da misalin ƙarfe 2:00 na rana

Tun farko an bayyana cewar saurayin ya shafe kimanin shekaru 13 yana ɗawainiya da yarinyar tun shekara ta 2014 ya kammala karatun NCE yana jiran ya samu aikin yi bai samu ba sai a watan daya gabata ya tafi neman kuɗi jihar Legas bayan ya dawo a daren jiya sai ya samu labarin cewa

Za'a ɗaura auren budurwar sa da wani ma'aikacin NNPC wanda suka haɗu da budurwar ƙasa da mako guda inda ya ce shi zai ɗauki nauyin komai, yanzu haka dai an ɗaura auren, kunji fa kuna ganin iyayen budurwar sun yi masa adalci kuwa?

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home