Wednesday, July 19, 2023

SABUWAR GUGUWAR RAƊAƊIN TSADAR RAYUWA: Litar fetur ta koma N617 a gidajen man NNPC











An shiga gagarumar tsadar fetur, har ta kai farashin litar fetur ɗaya a gidan mai na NNPCL.

Haka ya tabbata a FCT Abuja da kewaye, a ranar Talata.

Wakilin mu ya ga ana sayar da lita ɗaya 617 a Wuse da kewaye. Lamarin ya faru wata ɗaya bayan da aka cire tallafin fetur, da lita ɗaya ta kai 537.

A wasu yankunan cikin jihohi lita ɗaya ta tafi har 568. Mai magana da yawun NNPCL, Garbadeen Mohammed, ya ce a ba shi lokaci, zai yi bayani.

Wannan kari ya zo lokacin da yawan fetur ɗin da ake saye a kullum a Najeriya ya ragu da kashi 35 bisa 100.

Shugaban MDPPRA, Ahmed Farook, ya ce a yanzu fetur ɗin da ake saye a kullum lita Milyan 46.38 ne. Kafin cire tallafin fetur kuwa, a kan sayar da lita miliyan 65 ce a kullum.

Ya ce daga cikin waɗanda aka ba lasisin shigo da fetur, kamfanoni 3 ne kaɗai su ka shigo da fetur.

Tsadar fetur ta sake matsa lamba a lokacin da gwamnatin Bola Tinubu ke shirin bayar da tallafin kuɗaɗe domin rage wa marasa galihu raɗaɗin tsadar rayuwa.

A cikin ƙasa da dama sun koma shiga motocin haya saboda tsadar fetur.

Wasu kuma cewa su ke yi wannan tsadar rayuwa za ta iya yin tasirin da matasa za su ƙara shiga ruɗanin tafka laifuka a cikin al’umma.


0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home