Sunday, July 23, 2023

Hukumar NEMA Ta Ankarar da Al’ummar Neja Kan Ambaliyar Ruwa a Kananan Hukumomi 11 Read more: https://hausa.legit.ng/news/1545345-hukumar-nema-ta-gargadi-alummar-neja-kan-ambaliyar-ruwa-a-kananan-hukumomi-11/











Hukumar NEMA ta ankarar da al'ummar jihar Neja cewa za su fuskanci ambaliyar ruwa sosai a wasu kananan hukumomi 11 Lamarin zai fi kamari a kananan hukumomin Mokwa, Shiroro, Lavun da Borgu, yayin da zai kasance tsaka-tsaki a Edati, Gbako, Wushishi, Rafi, Mashegu, Magama da Agrana An umurci mazauna yankunan kogi da su gaggauta barin wajen domin neman tudun tsira domin dai kogunan na dab da batsowa sakamakon cika da suka yi Read more: https://hausa.legit.ng/news/1545345-hukumar-nema-ta-gargadi-alummar-neja-kan-ambaliyar-ruwa-a-kananan-hukumomi-11/



Kananan hukumomi 11 za su fuskanci ambaliyar ruwa daga Yuli zuwa Nuwamba Zainab ta bayyana cewa hasashe ya nuna cewa kananan hukumomin Mokwa, Shiroro, Lavun da Borgu na cikin rukunin yankunan da ke cikin hatsarin fuskantar ambaliyar ruwa a jihar kuma ana sa ran za su fuskanci matsanancin ambaliyar ruwa a cikin watannin Yuli zuwa Nuwamba. DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka Ta ce kananan hukumomin Edati, Gbako, Wushishi, Rafi, Mashegu, Magama da Agrana na cikin rukunin da za su fuskanci matsakaicin ambaliyar ruwa, cewa mazauna yankin za su yi fama da ambaliyar ruwa sosai daga Yuli zuwa Nuwamba. “Ya kamata a lura cewa jihar Neja ta riga ta fara fuskantar ambaliyar ruwa da iska mai karfi a wasu daga cikin wadannan yankuna don haka akwai bukatar al’ummar jihar su yi taka-tsan-tsan don gujewa asarar dukiyoyi da asarar rayuka,” inji ta. Read more: https://hausa.legit.ng/news/1545345-hukumar-nema-ta-gargadi-alummar-neja-kan-ambaliyar-ruwa-a-kananan-hukumomi-11/

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home