Saturday, July 22, 2023

Gobara Ta Lakume Shaguna 150 a Kasuwar Yan Katako Da Ke Zariya.











Mumunar gobara ta yi barna a kasuwar yan Katoko da ke yankin Zariya a jihar Kaduna a ranar Laraba.


Wutan da ya fara ci tun daga tsakar dare har zuwa wayewar gari ya kona shaguna 150 kurmus.

Hakazalika an yi hasarar dukiya na miliyoyin nairori a gobarar da ta tashi sanadiyar fadowar wayar lantarki.



Kaduna – A kalla shaguna 150 ne suka kone kurmus sakamakon gobara da ta tashi a kasuwar Yan Katako da ke Sabon Gari da ke yankin Zariya, jihar Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewar gobarar da ta fara ci daga karfe 1:00 na tsakar daren jiya ta dungi ci har zuwa rana.

Hamisu Buhari, babban jami’in tsaron kasuwar, ya ce gobarar ta fara ci ne lokacin da aka dawo da wutar lantarki sannan igiyar wuta ta fada kan rufin daya daga cikin shagunan.


Gobarar ta yadu zuwa sauran shaguna da ke kasuwar.”

Buhari ya ci gaba da bayyana cewa duk kokarin da aka yi na jan hankalin hukumomin kwana-kwana a yankin ya ci tura.

Ya ci gaba da cewa:

“Ni da kaina na je ofishin kwana-kwana na Kofar Doka. An sanar da ni cewa motar aikinsu ya lalace.

Sai na garzaya sansanin Kongo da ke jami’ar Ahmadu Bello inda aka fada mani cewa an umurcesu da kada su yi aiki a wajen harabar jami’ar.

“A karshe na kira ofishin kwana-kwana na ainahin kasuwar Sabon Gari. Sun bukaci na samar da man fetur wanda na aikata hakan kafin suka amsa mani.”

A wata hira da aka yi da shi, shugaban kungiyar masu katako a kasuwar, Alhaji Alin Ashiru, ya ce lamarin ya afku ne a ranar Laraba, rahoton The Cable.

Ya bayyana cewa shaguna fiye da 150 ne suka kone kurmus kuma cewa dukiyoyi na miliyoyin naira sun lalace.

Da aka tuntube shi, shugaban sashin kula da harkokin KEDCO, Abdul Azeez Abdullahi, ya karyata cewar tartsatsin wutar lantarki ne ya haddasa annobar.

Ya ce rahotanni da aka samu sun nuna cewa gobarar ta fara ne a daya daga cikin shaguna a kasuwar.

Hakazalika, Umar Mohammed, shugaban hukumar Kwana-kwana, Kofar Doka, Zaria ya ce motarsu bata aiki ne saboda hatsarin da ta yi kwanan nan bayan aikin ceto a wajen ajiyar mai na rundunar sojin Najeriya.

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home