Monday, January 1, 2024

Zanbada Naira Milion 1 Ga Duk Wanda Yakawo Mana Inda Manzon Allah Yayi Wa’azin Kasa – Imam Dr. Hamza Assudaniy Zaria











Zanbada Naira Milion 1 Ga Duk Wanda Yakawo Mana Inda Manzon Allah Yayi Wa’azin Kasa – Imam Dr. Hamza Assudaniy Zaria


Wani Malami a Zaria Imam Dr Hamza assudaniy zaria yana ƙalubalarntar masu wa’azin kasa kungiyar izalatul bidi’a wa’ikamatus sunnah cewa a kawo mishi inda manzon Allah (s.a.w) yayi wa’azin kasa…..


A cikin wannan sati ne da kungiyar izalah ƙarƙashin jagoranci Sheikh Abdallah bala lau sunka shirya wa’azin kasa a garin zaria da ke jihar kaduna wanda an shafe shekaru kusan takwas rabo da ayi wa’azin kasa da kasa a cikin garin zaria.

Shine yanzu muke samun wani labari inda wani malamin yake ƙalubalarntar wa’azin kasa da kungiyar izalatul bidi’a wa’ikamatus sunnah suke shiryawa a matsayin bidi’a amma suke cewa sune yan bidi’a masu Maulidi.

Malam Imam a Sheikh ya fitar da Wannan abun ne a shafinsa na facebook mai suna Imam Dr.Hamza Assudaniy, inda yake cewa.

“Anata Bidi’antar Da Murnan Samun Manzon Allah Wanda Akafi Sani Da (MAULIDI) Ga Babban Bidi’a Na Kewaye Daku

Wa’azin Kasa Bidi’a Ne Annabi Bayyiba Sahabbai Basuyiba Tabi’ai Da Tabi’ut Tabi’una

Tabbas Idan Baku Kawo Mana Inda Sayyuduna Muhhammadu Rasulullahi Yayi Ba Kun Tabbatar Mana Ku Yan Bidi’a Ne

Muna Rokon Allah Ka Dauwamar Damu Cikin Soyayyar Manzon Allah”

A yau ne ranar Assabar kungiyar izalatul bidi’a wa’ikamatus sunnah sunka shirya wa’azin kasa da kasa a cikin garin zaria , da za’a gudanar a yau kamar yadda shafinsu sunka wallafa sun kamala shirye shirye tsaf domin fara wannan karatu.

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home