Tuesday, January 23, 2024

Rigima ta sanya yayi Ajalin Abokin aikinsa a kano











Rigima ta sanya yayi Ajalin Abokin aikinsa a kano



Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama wani matashi mai suna Isma’il James, dan shekara 32, bisa zarginsa da kashe abokin aikinsa a cikin kamfanin sarrafa Buhuna Fas Agro, dake rukunin masana’antu a unguwar Sharada dake jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan SP Abdullahi Kiyawa ne ya sanar da hakan ga gidan rediyon Dala FM kano, da yammacin Lahadin nan, ya ce matashin James ana zarginsa ne da kashe abokin aikin nasa mazaunin unguwar Ja’en Dango dake karamar hukumar Gwale, mai suna Tukur Adamu dan shekara 32, bayan da suka samu rikici a kamfanin.


Isma’il James ya kashe abokin sana'ar sa daga husuma wanda yanzu dai abokin nasa Tukur Allah yayi masa cikawa.......

 

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home