Saturday, December 30, 2023

Saurayina ya fasa aure na saboda na faɗa masa gaskiya cewa an taɓa yi min fyaɗe—Hadiza











Kwamitin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugabancin ƙasa na am’iyyar APC ya koka kan kafafen yaɗa labaran karya da ake zargin jam’iyyar adawa ta PDP na amfani da su wajen ɓata sunan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar mai mulki, Bola Tinubu.


Wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na kwamitin, Bayo Onanuga, ya fitar, ta ce PDP ta samar da wani gungun masu yaɗa farfaganda a hedikwatar ta ta kasa dake gidan Wadata da ke tsara labaran ƙarya a kan Tinubu.


Muna so mu fadakar da ƴan Najeriya kan irin munanan yunkuri da kuma tsare-tsaren da jam’iyyar adawa ta PDP ke fitar wa na yaɗa labaran karya, musamman cikin harshen Hausa domin ɓata sunan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da APC a idon ƴan Najeriya.

“Wannan kamfen din na PDP tuni an kammala shi tare da tawagar matasa da ka aiki dare da rana daga hedikwatar PDP ta kasa da ke Wadata House, Abuja.

“Jam’iyyar ta kuma dauki masu amfani da kafafen sadarwa domin gudanar da farfaganda ga Tinubu.

“Mun bankado wannan mugunyar makircin da aka yi niyya don murkushe ‘yan Najeriya da ma ’yan Arewa musamman ’yan Arewa don ganin an yi wa Asiwaju Bola Tinubu mummunan zato a matsayin hanya daya tilo da jam’iyyar PDP da yakin neman zabenta na shugaban kasa za su samu dama a zaben shugaban kasa da za a yi a ranar 25 ga Fabrairu.

“Muna ganin ya zama dole a wannan lokacin don mu fito da wannan makircin ga ƴan Najeriya don su gane gaskiya,” in ji shi.

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home