KADA KA KASAKE KAYI AURE HAR SAI KA MALLAKI WA DANNNAN ABUBUWAN: Dayawa suna aure sai kuma su kasa rike auren. Duk kudin da zaka kashe wajen auro mace, bai kai kudin da zaka rika yin dawainiyar yau da gobe ba. Wannan yasa idan har ka kasa mallakar wasu abubuwa gara ka hakura da auren saboda ko kayi baza ka morewa auren ba. Ga wasu abubuwan da ya kamata ka mallakesu kamin ka soma tunanin yin aure.
1: Illimin Neme Da Zaman Auren:
Dole ne ka samun illimin yadda zaka samo macen da kake so ka aura, da kuma illimin sanin yadda zakayi zaman auren da ita.
Kashi 60 cikin 100 na mazan da suke aure basu da wannan illimin kuma basa neman sanin illimin. Tunda sunga kowa yana shiga a hakan suma kawai sai su fada a hakan. Daga karshe zaman auren ya kasa dadi sai kuma saki.
Don haka tabbatar da cewa kamin kayi aure ka samun wadannan illimin domin ka amfani kanka.
2: Abun Yi:
Bama kawai abun yi ba, ka tabbatar wannan abun da kake yi kana samun abunda kake ganin zaka iya kula da iyayenka da kuma iyalanka. Kada ka dauko aure saboda kana wani aiki ko sana’ar da kai kanka bazaka iya rike kanka da shi ba bare kuma matar da zaka aura.
Mutane dayawa suna daukar cewa, da zaran sunyi aure nauyin iyayensu ya tashi daga kansu. Wannan ba gaskiya bane. Ubanka ko Dan Gote dole ka kula da lafiyansa, wajen kwanansa, suturansa da kuma abincinsa. Wannan wajibi ne akanka har sai idan shine ya sauwaka maka yin hakan. Amma idan kana neman gamawa da duniya lafiya zaka so ka yiwa Iyayenka wannan hidimar kaman yadda Allah SWT Yace.
Rashin sanin hakan yasa wasu da zaran sunyi aure sai su maida hankalinsu akan Iyalansu kadai su manta da iyayensu. Ka tabbatar da cewa abunda kake samu ya isa ka kula da iyayenka da iyalanka kamin ka tinkari yin aure.
Ka sani, Allah bazai tambayeka mai yasa baki yi aure ba idan ka mutu babu aure. Amma zai tambayeka yadda ka kula da iyayenka da kuma iyalanka idan kayi aure. Don haka ya zameka wajibi ka samu abunda zaka iya hidimar wadannan bangarorin biyu
3: Lafiya:
Kuskure ne babban ka yi aure bayan kasan baka mallaki lafiya ba.
Ana samun mazan da suna sane gabansu baya aiki ko yana da rauni amma a hakan suke zuwa su nemi aure kuma a basu.
Akwai masu matsalar kwakwaluwa har ma da cutar kanjamau.
Don haka yake da kyau ka mallaki lafiyar kamin kace zaka yi aure, domin rayuwar aure na mai lafiya ne.
4: Hakuri;
Kada ka sake kayi aure muddin idan kasan mara hakuri ne kai. Domin zaman aure gaba dayansa na masu hakuri ne.
Zaman aure za a bata maka kaima zaka bata mata. Wannan yaza dole ka tabbatar zaka iya hakuri da wasu abubuwa da zasu taso idan ba haka ka rika aure kenan har sai bayan ranka.
5: Ka Mallaki Zuciyar Tinkaran Kalubale:
Zaman aure akwai kalubale na rayuwa da dama da suke iya tasowa mutum bayan aurensa. Ka tabbatar idan hakan ya taso zaka iya fuskantar matsalar ba gudun matsalar ba.
Kana Iya samun kanka cikin wadata kamin kayi aure, bayan aurenka sai abubuwan su sauya. Ka dawo abinci da gidan haha su gagareka biya. Ga yara, ga iyaye ga kuma mata da ciki. A irin wannan yanayin kana bukatar jimriya da karfin halin da zaka tinkari wannan lokacin kamin Allah Ya kawo karshensa. Muddin baka mallaki wannan zuciyar ba, zaka gudu ne ka bar iyalanka ko kuma kace zaka yi saki. Wanda ba hakan aka so ba.
Da fatan maza musamman samari zasu yi kokarin mallakana wadannan abubuwan kamin su tinkari yin aure.
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home