Thursday, December 28, 2023

Me ya sa Real Madrid ta hana rubuta sunan Mbappe da Haaland a jesinta?











Me ya sa Real Madrid ta hana rubuta sunan Mbappe da Haaland a jesinta?


Kulob din Real Madrid na Sifaniya ya haramta wa magoya bayansa su nemi a saka musu sunayen ɗan ƙwallon PSG, Kylian Mbappe, da Erling Haaland na Man City, a rigunan da ake sayarwa a shagon kulob din.

Daga yanzu Real Madrid ba za ta amsa bukatar rubuta sunan Mbappe da Erling Haaland a jesin, kamar yadda rahoton ya bayyana.

Magoya bayan Madrid da za su sayi rigunan kulob din, za su iya neman a sanya suna da lambar a bayan rigar. Amma shafin Goal.com ya ruwaito rediyon SER Deportivos za a ki karbar bukatar rubuta sunan Mbappe ko Haaland.

Gidan rediyon ya tabbatar da wannan batun a wajen magoya bayan kulob dinsu biyu, wadanda suka nemi a rubuta sunayen 'yan wasan da aka haramta.

Ma'aikatan shagon suka ce musu ba za su iya rubutawar ba saboda Mbappe da Halland ba 'yan wasan ba ne. Wani dalilin shi ne matsalolin dokokin hakkin hoto sun haramta musu sanya sunan 'yan wasan wasu kulob din.

Amma me ke janyo magoya bayan Madris suke neman sanya sunayen Mbappe da Haaland a rigunansu? Wani dalili shi ne an dade an rade-radin cewa Real Madrid suna da niyyar sayan manyan 'yan wasan biyu.

Sai dai ganin yadda tauraruwan Haaland ke haskawa a Man City, da wuya kungiyar ta sayar da shi nan-kusa. Amma akwai yiwuwar PSG ta sayar da Mbappe a karshen kakar bana.

Haka nan rahotanni sun nuna cewa a wannan wata Madrid ta shirya gabatar da tayin sayan Mbappe a watan Janairu. Amma kuma za su ba wa PSG har zuwa 15 ga Janairu ne su amsa tayin.

Matukar PSG ba ta amince da tayin ba, Madrid za ta koma ga dan wasan Man City, Haaland don gwada sa'arta.

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home