Thursday, December 28, 2023

Dalilin da yasa amarya ke kwanciya tace bata da lafiya da zarar ango ya dawo daga rakiyar abokansa











Dalilin da yasa amarya ke kwanciya tace bata da lafiya da zarar ango ya dawo daga rakiyar abokansa



Kashi 85% na angwayen da aka ji ra'ayoyinsu sun bayyana damuwarsu kan yadda suke hanƙoron saduwa da amarensu a daren farko amma sai amaren su ɓullo musu da wata kisisina suce kansu ke ciwo ko kuma suce basu da lafiya ko jini suke, waɗannan sune dabaru ukku da mafi akasarin amare ke amfani da su wajen hana angwayensu saduwa dasu a daren farko


To sai dai angwayen suna bayyana damuwarsu wasu a fili wasu kuma a ɓoye ganin cewa wani angon da zarar abokansa sun rako shi ɗakin amaryar har ƙagara yake su gama jawabinsu su fita ga danƙwaleliyar Kaza ya siyo suci tare da amarya amma da zarar ya rakasu ya dawo ya rufe ƙofa sai kawai ya ganta a kwance kuma tayi masa ƙaryar rashin lafiya, game da wannan matsalar anji ta bakin ƴan mata kuma sun bayya dalilan da kesa suna yiwa angwayensu haka




Sai dai masu mazan suna da ra'ayin cewa ba zasu tilastawa amaryarsu dole sai sun sadu da ita ba a daren farkon ba inda wasu ma ke cewa zasu iya lallaɓa ta har zuwa mako guda, ko kana ɗaya daga cikinsu?

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home