Thursday, August 10, 2023

Mutum 15 Sun Mutu, 5 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Kogi......











Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC), ta tabbatar da mutuwar mutane 15 tare da jikkata wasu biyar a wani hatsarin mota da ya afku a Jihar Kogi.




 







Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN), ya ruwaito cewa hatsarin ya faru ne tsakanin J-5 Boxer bas da wata tankar mai, a Koton-Karfe kan babbar hanyar Lokoja zuwa Abuja da misalin karfe 7:30 na safiyar ranar Talata.


Kwamandan FRSC a Kogi Stephen Dawulung, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an garzaya da mutanen biyar da suka jikkata zuwa asibitin Ideal da ke Koton-Karfe domin ba su kulawar gaggawa.







 







Dawulung, ya ce an ajiye gawarwakin wadanda suka mutu a dakin ajiye gawa na babban asibitin tarayya (FMC) da ke Lokoja.



 







Kwamandan sashen, ya bayyana cewa musabbabin hatsarin ya faru ne saboda keta dokokin hanya da direban motar bas din ya yi, wanda ya ke tukin mota a lokacin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa Abuja daga Lokoja

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home