Sunday, February 18, 2024

TIRƘASHI: An Nemi Murja Kunya An Rasa A Gidan Yarin Da Take Tsare











TIRƘASHI: Duk iskancin Murja Kunya mutuniyar kirki ce kuma ta tsira saboda tana son Shehu Ibrahim Inyass, -Alhaji Anisee Futuhi

Wani masoyin Sheíkh Ibrahim Inyass Alhaji Anisee Futuhu ya bayyana cewa duk kallon ƴar iska da mutane suke yi wa jarumar Tik-Tok murja Ibrahim Kunya shi a wajensa saliha ce kuma yana sonta saboda masoyiyar Inyass ce, "ko da sheɗan ne yake son Inyass ni ma ina son sa balle kuma Murja Kunya". In ji shi.

Futuhi ya bayyana haka ne ta cikin wani bidiyo wanda Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta samu, inda ya ƙara da cewa "Shehu Ibrahim Inyass ya ce duk wani ɗan iska da mutumin banza ba sa son sa, duk wanda aka ga yana sonsa to mutumin kirki ne. Yadda na tsarkaka haka na tsarkake masoyana gabaɗaya. Saboda haka, ko da duk Duniya babu wanda ya kai Murja Kunya iskanci ni a wajena mutuniyar kirki ce, malama, kuma sayyada, duk iskancinta ta tsira saboda masoyiyar Shehu Ibrahim Inyass ce". A cewarsa.

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home