Sunday, January 21, 2024

“Da zuciyarka ta mutu gwara gabanka ya mutu”— In ji Mariya











Hausawa kan ce mata adon gari in baku ba gari shafukan sada zumunta na zamani wato Social Media na cigaba da ɗaukar hankali masu amfani da su inda wasu ke amfani da kafafen sada zumuntar wajen jan hankalin mabiyansu.

Wata matashiya mai suna Mariya mai laƙabin Mpreety a dandalin sada zumunta na Twitter ta bayyana cewar “Da zuciyar ka ta mutu gwara gabanka ya mutu” rubutun nata dai ya jawo hankulan mabiyanta a dandalin inda wasu da suka fahimci abinda ta faɗa gaskiyane suka goyi bayanta wasu kuma akasin haka, ga hoton rubutunta nan daga ƙasa.

A wani labarin kuma

Malamin Addinin Kirista Adebayo ya bayyana Abubuwan da zasu faru a Shekarar nan.

Fasto Adebayo ya bayyana abubuwan da zasu faru a cikin wannan shekara ta 2023.

Babban mai kula da cocin Remdemed Christian Church of God (RCCG).pasto Enoch Adejere Adebayo, ya bayyana wasu abubuwa da ake tsammani a shekaran 2023.

Adebayo yayin hidima a majami’a ya gayawa ikilisiyarshi da su kula da samun karin damammaki a 2023.

Ya bayyana hakane a lokacin da yake fitar da sakon na shekaran 2023, inda ya kara da cewa za’ayi musayan arziki.

Babban malamin addinin ya kumace duniya zata samu zaman lafiya a bana.

Adebayo yace, yanayin zaiyi kyau a wasu wurare amma munada imanin cewa Allah zaiyi mana maikyau a duk inda muke.

Allah kuma yace a wannan shekara za’afi zaman lafiya.

Rahoto Hajiya Mariya Azare.

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home