Ya kamata gwamnati taci tarar duk namijin da ya saki matarsa – Mansurah Isah
A yau tsohuwar Jarumar Masana’atar Kannywood mansurah isah tsohuwar matar jarumi sani musa danja tazo da wani babban magana a kafar sada zumunta akan saki.
Mansurah Isah tazo da magana akan yawan sakin da akeyi a afrika domun su turawa sun fi mu adalci mu musaulmai saboda yawan saki kamar anfi yinsa babu ka’ida saboda akwai tsari wanda ankace idan mace ta nemi saki a biyata kuɗin sadakinta.
“A nawa sani musulunci yace mace tayi idda a gidan mijinta tayi jini ukku tana yiyuwa idan naso sai ya mayar da ita amma idan ya bani har ta gama jini ukku dole sai ya sake biyan sadaki in ba saki ukku ba kenan.amma da wuya mutum ya saki Matarsa yayi mata adalci.
Ni naga wanda ya saki matarsa ya bata gida ya bata mota kuma duk wata yana bata albashi kuma ya saketa,amma ya gayamata duk ranar da kinka yi aure bakin wannan lokacin zan janye miki duk wannan Jindadi domin ni ba muharaminki bane ni kuma ta yadda idan bata da lafiya shine ke kula da ita ya kaita asibiti yabiya kudin komai har lokacin da tayi aure kuma gida da motan da ya bata bai amshe ba.
Ya barmata halak malak sai dai ciyarwa kuɗin magana ya daina duk wani sada zumunta da magana sunka daina idan ma wani abu ya tashi na yayansu sai yayiwa mijinta magana yasan abinda zaiyi.
Amma ni bani mamaki kuma gwamnati basa cewa komai inason ta maida hankali wajen sakin yaya mata da akeyi ayiwa yarinya sakin wulakanci kuma naira goma baza’a bata ba, kuma kafin ya aure ta ya hanata aiki, ya hanata hulda da yan uwanta da iyayenta zai hanata sana’a daga karshe kuma yayi mata sakin wulakanci.
Wani ma cewa zaiyi sutura/tufaffin da ke jikinta ta tuɓe su nashi ne, wani kuma matar bata yi masa laifin komai ba kawai ji yake ta ishe shi kawai yana son sabon jini.
Amma yanzu wallahi abinda matasan mu maza abinda sukeyi bai dace dan Allah malaman mu a kawo wani law ko ka’ida ina tunanin idan ankace idan mutum ya saki mace za’a ciri wani abu a cikin dukiyarsa ina tunanin zai rage mutuwar aure da akeyi, sai ace idan ka saki mace ga abinda gwamnati zata cazeka ko kuma ke mace idan kice zaki rabu da miji ga wani abu da za’a cazeki amma sai da kwawaran hujja.”
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home