Friday, December 1, 2023

TURNUƘU A TARABA: 'Yan bindiga sun bindige maharba 18 a gumurzun yunƙurin afkawa garin Bali







Aƙalla maharba 18 ne suka rasa rayukan su a wani gumurzu da ‘yan bindiga, a hare-hare biyu da aka kai wa garin Bali, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Bali a Jihar Taraba.


PREMIUM TIMES ta samu bayanin cewa an kashe maharba 15 a gumurzun su da ‘yan bindiga a ranar Talata da dare, a tsaunin da ke kusa da garin Maihula.


Sauran ukun kuma an kashe su ne a wani kwanton-ɓauna da ‘yan bindiga suka yi wa maharban kusa da garin Dakka.


PREMIUM TIMES ta ji cewa ‘yan bindiga sun yi ƙoƙarin kutsawa garin Bali, ko ta halin ƙaƙa, amma sai maharban suka yi gumurzun zaɓen taho-mu-gama da su.


Maharbar da ke da sauran kwana a gaba, sun tsere da raunuka a jikin su.


Majiya mai suna Musa Umar, ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba cewa ‘yan bindigan sun bindige dakarun maharba 14 nan take.


Ya ƙara cewa yayin da ɗaya ya rasu a kan hanyar garzayawa da shi zuwa asibiti.


Basaraken Bali, wanda ke riƙe da sarautar Kur na Bali, Mahamud Abubakar, ya shaida wa manema labarai cewa maharbar da aka kashe, dukkan su sun rasa rayukan su ne a ƙoƙarin hana ‘yan bindiga kutsawa cikin garin Bali.


“Sai dai abin takaici yaƙin ya ci maharban saboda ‘yan bindiga sun fi su makamai masu ƙarfi.


Shugaban Maharba na Jihar Taraba, Adamu Ɗantala, ya tabbatar da kisan maharba 15.


Ya yi kuka roƙo ga gwamnati a kai masu ɗaukin shawo kan matalsalar tsaro, musamman ganin ko a makon da ya gabata, sai da ‘yan bindiga suka kashe mutum 12 a cikin Ƙaramar Hukumar Ussa 

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home