Thursday, November 30, 2023

Abubuwan dake kashe batirin waya..

 








Abubuwan dake kashe batirin waya..


Batirin waya na Lithium-ion batteries wanda yawanci yake zuwa a smartphones da muke amfani dasu yanada Limited na raguwar karfin shi wurin amfani.


Tabbas yawan yin amfani da waya yana degradation na karfin battery, wannan kuma usual abu ne, wanda ya zama dole kayi amfani da wayarka tunda kudi kasa kasiya domin tayi maka amfani.


Amfani da Charger mai karfi wacce ba ta wayar da kasiya ba, yana illata batirin waya cikin lokaci, saboda karfin cajin yana shiga batirin ba daidai yadda aka tsara batirin ba, dan haka yakeda muhimmanci kadinga saka wayarka caji da ainahin charger da kasiya wayar da ita, ko caji zaka kai wurin masu caji ka hada da charger naka.. Yin amfani da wata Charger mai saurin cika waya har kaji wayar tana zafi a lokacin da take caji, hakan ba birgewa bane indai ba charger din na wayar bane.


Idan wayar da kasiya Second Hand ce ko kuma asalin Charger na wayar ya bata, zaka iya searching ko a google ne su baka sunan ainahin Charger na wayarka, a duk sanda katashi siyen Charger din sai kaje shagon mai siyarwa kace mashi ga kalar charger da kake bukata.


Wasu idan sun saka wayarsu a caji kuma wayar ta cika tayi Full, maimakon su cire daga charging sai suki cirewa, wanda hakan kuskure ne sosai, barin waya a jikin Caji bayan ta cika zaiyi stressing batirin, anyi designed wayoyin ne su dauki cajin da yakai 100% kadai, idan kabarta tana caji bayan takai wannan Percentage din zai iya kashe batirin wayar.


Rashin saka waya caji har sai ta dauke da kanta shima yana kashe batiri sosai yana zama detrimental, shiyasa yakeda muhimmanci da zaran wayarka takai 15% kome kakeyi da ita kayi hakuri kaje ka sanya a caji.


Cika hasken screen na waya yana shan caji sosai ba kadan ba, yanada kyau ka rage hasken screen na wayarka hakan zai taimaka wa batirin wurin karko da kuma rage saurin karewa.


Akwai irinsu Background Apps din nan duka sai ka tsayar dasu kayi disable nasu a wayarka idan bahaka ba suma shan caji suke sosai batareda kasani ba.


©Dr. Salisu Abdurrazak Saheel

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home