Wednesday, December 20, 2023

Maryam Yahaya ta bayyana kalar mijin da take son samu kafin tayi aure












Maryam Yahaya ta bayyana kalar mijin da take son samu kafin tayi aure


Jama’a da dama musamman masu sha’awar kallon fina finan Hausa na masana’antar Kannywood na bayyana mabambantan ra’ayoyinsu akan jaruman masana’antar musamman mata.


Inda wasu ke cewa aure ne yafi dacewa dasu fiye da suzo suna yin shirin film yayin da a nasu ɓangare jaruman ke bayyana cewa Allah bai kawo lokacin auren ba don shi aure lokaci ne.

A nan shahararriyar jarumar masana’antar ce Maryam Yahaya tace ita fa sai ta samu namiji mai riƙo da addinin musulunci da ilimi m, tsafta da tsoron Allah wanda zai riƙeta bisa gaskiya da amana sannan za tayi aure.

A wani labarin kuma.

A yunƙuri uku, majalisar wakilan Amurka ta kasa zaɓen shugaba

Majalisar Wakilan Amurka ta ɗage zamanta cikin yamutsi bayan yunƙurin da ta yi har uku na zaɓen Kevin McCarthy na jam’iyyar Republican a matsayin shugaba, ya ci-tura.

Wannan shi ne karon farko a ƙarni ɗaya da aka kasa zaɓen a ƙuri’ar farko.

Dan majalisa McCarthy, daga California, ya kasa samun rinjayen yawan kuri’un da ake bukata, 218, bayan da ‘yan majalisa 28 na jam’iyyarsa ta Republican suka juya masa baya, inda suka gwammace su zaɓi Jim Jordan a maimakonsa.

Sai dai duk da haka Mista McCarthy ya ce zai ci gaba da takarar har sai ya yi nasara.

A baya shi ne shugaban marasa rinjaye na majalisar, saboda haka ake sa ran ya zama kakakin a yanzu bayan da ‘yan Republican ɗin suka karɓe rinjaye da majalisar a zaɓen rabin wa’adi na watan Nuwamba.

Amma kuma idan aka ci gaba da rigima a takarar, to hakan zai tilasta wa ‘yan majalisar su nemi wani ɗan takarar daban.

Tasirin wannan koma bayan shi ne babu wani aiki da majalisar za ta iya gabatarwa har sai ta naɗa kakakinta.

A majalisar dattawan ƙasar kuma, ‘yan jam’iyyar Democrat mai mulkin ƙasar ke da rinjaye, abin da ke nufin ba lalle ne mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris ta ci gaba da kaɗa kuri’arta ba a duk lokacin da wani batu da ke gaban majalisar ya gamu da cikas.

Saboda a yanzu ‘yan Democrat ɗin na da ƙarin ƙuri’a guda da suka samu a zaɓen watan Nuwamba da aka yi a faɗin ƙasar.

Ƙarin Labari.

Masu satar mai ne su ka haddasa fashewar tankar mai a Ogbomoso — Hukumar kwana-kwana

Hukumar kashe gobara ta jihar Oyo, ta ce satar mai wasu ɓatagari su ka yi daga wata tankar man fetur da ta fadi, su ne su ka haddasa gobarar da ta tashi a ranar Lahadi a garin Ogbomoso.

Daraktan ayyuka na hukumar, Ismail Adeleke, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya cewa wani Samuel a ranar Lahadi da misalin karfe 12:41 na rana ya kai rahoton lamarin a ofishin hukumar na Ogbomoso.

“Nan da nan, mu ka dauki adireshin wurin, mu ka kuma tura jami’an kashe gobara karkashin jagorancin ACFS Olayiwole wajen wutar ba tare da bata lokaci ba, a nan gaban Cocin Winner, Isale General, Ogbomoso.

“Da isowar jami’an rundunar kashe gobarar su ka fara aiki tare da kashe wutar gaba daya,” in ji Adeleke.

A cewarsa, binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa gobarar ta afku ne sakamakon wata tankar man fetur da ke dauke da lita 33,000 na wacce kai ya kwace ta fadi a gefen titi.

“Sannan kuma daga baya ta kama wuta saboda haramtattun ayyukan wasu jama’a da ke kokarin dibar man fetur,” inji shi

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home