Sunday, August 20, 2023

An gano ƙofar (Gate ɗin) Jahannama. Kalli cikakken video 👇











An gano ƙofar (Gate ɗin) Jahannama.

Scientist na iƙirarin cewa sun gano gate ɗin Jahannama a wata ƙasa Turkmenistan, wanda idan ka bi wannan Gate ɗin zai kai ka har zuwa Jahannama.

Ramin ƙaton rami ne yafi girman Stadium, wuta ta haura shekara hamsin (50) tana ci a wannan rami, tsofaffin garin sun tabbatar da sun taso sun tarar da wannan wuta tana ci a wannan waje kuma har yanzu tana ci gaba da ci wannan wuta.

A wani ɓangaren kuma wasu mutane na cewa, wannan ba hanyar Jahannama bane, lokacin da sojojin Soviet, wato Rasha da suke haƙe-haƙen su, lokacin ne suka haƙo wani “Gas” mai ƙarfi, bayan sun haƙo shi ne suka rasa yadda za su yi dashi, shi ne suka kunna ashana suka cinna masa wuta da nufin zai ƙone ya rage ƙarfi, to shi ne da yake da Gas a wajen har yanzu bai daina ci ba.

Idan ba a manta ba sojojin Soviet sun haƙa ramin da yafi ko wane rami tsawo a duniya, to an samu scientist ɗin da suka zura ‘Mic’ a cikin ramin suka jiyo wasu muryoyi wanda suka yi ikirarin cewa sun ji sautin Jahannama a ciki.

Ya kuke kallon wannan lamari.?

Daga Mustapha Muhammad.


0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home