Thursday, July 27, 2023

Sirrin maza wanda ya kamata kowanne namiji ya sani,domin gamsar da iyalin sa hadi na Musamman....












Sirrin maza wanda ya kamata kowanne namiji ya sani,domin gamsar da iyalin sa hadi na Musamman

 

 

Hakika namiji yana da wani sirrin Wanda ba kowacce mace ta San wadannan sirrin ba Sai wacce Allah ya sanar da ita, shi namiji ya kasance Mai tsanani son karairaya, rangwada, kissa,shagwaba, da kalaman soyayya, duk macen data San wadannan kuma take aikatasu hakika zata zama tauraruwa a zuciyar mijinta.


Babu KO shakka wadannan kam Na Daga cikin abubuwa mafi muhimmanci dake taka muhimmiyar rawa wajen sace zuciyar namiji ,ya kasance kin tanadi wani suna Na musamman da Zaki dinga kiran mijinki dashi kamar

 

● sweety

● honey

● darling

● Abin kaunata

● farin cikin rai Na.

 

Magana ta gaskiya a wannan fannin a nan ne aka yiwa matan hausawa nisa , don da yawa sune basu dauki hakan a wani Abu Mai muhimmanci dake Iya jefa tsantsar sonki a zuciyar mijinki ba.

 

Dole a matsayin ki Na macen da ke son ta mallaki mijinta saifa ta dage wajen Iya kalaman soyayya don sune masu kwantarwa da namiji hankali koda kuwa an bata masa rai KO hankalinsa ya tashi.

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home