Friday, March 1, 2024

Zanga-zanga ta ɓarke a garin Birci kan yawaitar hare-haren 'yan bindiga a ƙaramar













Zanga-zanga ta ɓarke a garin Birci kan yawaitar hare-haren 'yan bindiga a ƙaramar hukumar Kurfi da ke jihar Katsina 

Wasu fusatattun matasa sun gudanar da zanga-zangar rashin tsaro a garin Birchi bayan harin da Yan Bindiga suka Kai cikin dare a garin Wurma a karamar hukamar Kurfi da ke jihar Katsina. 

Katsina Post ta samu cewa wannan shi ne kusan karo na biyar a cikin sati guda da 'yanbindigar ke kai hari a garin wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama da kuma kona dukiyoyi a garin.

Matasan dai sun yi tsintsima a bisa titunan garin inda suke kiraye-kiraye ga Gwamnatin Katsina da ta gaggauta daukar matakin samar da zaman lafiya a yankin nasu.

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home