Thursday, February 29, 2024

Tsohuwar jarumar Kannywood Malika ta dawo film bayan mutuwar auren ta....











Tsohuwar shahararriyar jarumar fina finan Hausa na Kannywood, mai suna Maryam Malika, ta fito daga gidan mijinta inda ta koma shirin film.

Tsawon shekara da shekaru dai ba’aji duriyar jarumar ba sakamakon auren da tayi, sai a ranar Alhamis sashin Hausa na BBC yayi fira da ita inda ta bayyana mutuwar auren nata a matsayin kaddara.

A halin yanzu kuma ta dawo masana’antar Kannywood domin cigaba da taka rawa a fagen shirin film din hausa.



Malika wacce a baya ta kasance a kan gaba cikin jerin taurarin dake haskawa a masana'antar Kannywood, ta sake dawowa sana'ar Film bayan mutuwar aurenta

A ganinku menene dalilin da yasa auren ƴan film bai cika yin ƙarko ba?

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home