Saturday, January 13, 2024

Yar uwa kalli video Nan domin ki koyi yadda zaki tadawa maigidan ki sha’awa har ya gamsar dake

 







Zuwa gareku MAZA DA SABIN ANGW/AYE


Wani ne ya turomin sago akan zaiyi aure yana neman shawara da "dos and dont" na aure.


Naga ya dace in yi posting may be akwai wadda zasu amfana, duk da nasan abune mai wuya cikin dan gangani lokaci da rubutu a fadi abunda ke cikin aure tunda wani abun sai ka shiga zaka gani ko ka gane.


So below is what I send him :-




Ka sani aure ibadane a cikin dukkan ibada da ruyawar akwai jarrabawa a cikin sa, hakuri, kiyaye dokokin da Allah da koyi da sunnan Annabi zai kaika ga cin nasara a ciki.

Ka sani Amanace a wajen ka kuma Allah zai tambayeka akan amanar da aka damqama.

lyayenta sun baka ita ne dan kyauta zato a gareka akan 'yar su zata samu kuluwa da farin ciki a wajen ka, sabida haka kazama gatanta, karka sake ka samarmata da aqasin haka domin zai nuna gazawarka da qasqanci a matsayin ka na jagora.

Kiyaye dukkan hakkokinta da ya rataya akan ka.

Ka sani ita mace da kyauta da kyautata mu'amala aka fi sace zuciyarta, ka kasance mai kyautatawa a cikin kalamanka wajen mata gyara da kiyaye furta abunda zai cutar da zuciyarta, ka kyautata a cikin ciyarwa, tufatarwa, muamalantarta da 'yan uwanta.

Ka sani mace halittace mai taushi zuciya da raunin hankali, wani lokaci zakaga abunda kake so wani lokaci sai kayi hakuri matugar hakuri da kawaici da ita.

Ka sani kai jagora a gidanka dan haka dole ka

kasance abun koyi a cikin dabi'u da halaye a cikin gidanka. Kar ka bari munanan dabiun ka ya zama abun kyama da zargi a cikin gidan ka, matuqar baka kiyaye naka ba zaiyi matuqar wuya ta iya kiyaye nata, wadda yin hakan zai zama silar fititintunu a auren ku.

Kiyaye tsabtar jikinka, babu wadda yake son kusantar kazamin mutum, ka kasance mai kiyaye tsabtar jikinka a duk lokacin da zaka kusanci matarka, wannan zai samar mata da nitsuwa a zuciyarta da zata mu'amalance ka cikin kwaniyar aurenku cikin sauqi.

Bayan tsabta, askin sama da qasa da yin brush atleast safe da dare, Ka riqe turare dan shine zai zama dan sagonka zuwaga matarka cikin sauqi


Ka kiyaye shigan 'yan uwanka al'amuran rayuwar gidan ka ko tsakaninka da matarka, cikin saugi in baka iya tsayarda kowa a matsayar sa ba zaa dagulama lissafi da rayuwar gidanka akan abunda bai kai ya kawo ba a hanaka zaman lafiya da jin dadi da iyalanka.

A duk lokacin da kuka samu matsala ka bada kofar zama tattaunawa a tsakanin ku domin shine kofa mafi saugin samu gyara, mafita da maslaha a tsakanin maaurata.

Matarkace, ka karanceta kasan waye ita da yadda take muamalantar mutane, Karka bari wani ko was su zo suna fadama waye matarka domin aqasarin lokaci qarya ko sharrinta za'a fadama ba alkhairintaba.

Ka sani a cikin zamanku zakaga abunda baka so a game da ita, ka tuna itama haka zata gani akan ka, so kuyi hakuri akan wadannan ku na yawan tuna kyawawan halayen juna dan su zasu kasance abunda zasuna kawar muku da wadanchan munanan halayen.

Ka kasance mai kawaii kuma mai gyara a cikin gidanka ba mai dagula lissafiba.

Ka sani namiji mai wasa da raha da iyalansa yafi samun walwala da jin dadi a cikin aure fiye da miji mai tsare gida.

Ka kasance mai iya bada hakuri in kayi ma matarka kuskure domin yaf sauqi kuma yakan karka lagwan fitintunu da dama a tsakanin maaurata.

Ka sani yadda kake da hakki akan matarka wajen kwanciyar aure haka take dashi akan ka, karka kasance marowaci ko mai kauracewa matarka ba tare da dalilin da musulunci ya tanadarba dan akwai cutarwa a ciki sosal, kuma kofar bude fitinane sosai a aure da rayuwa duka.

Ka zaman to da ita abokiyar shawara ko da kuwa ba lallai kayi aiki dashi ba, yin hakan zai baka damar sanin irin hankali da tunaninta wadda zhakan zai baka damar mata gyara a cikin tunanin ta.

Ka zamto mai iya amsan uzuri domin shi dan adam ajine mai kuskure ne, kai ma zaka iya kuskure kuma zaka so tama uzuri. Kuma yin uzuri ma juna yakan rufe kofofin fitintunu da dama a aure.

Ka sani waya (phone) da social media yana daga cikin babban galubale da barazana da aure da dama ke fuskanta, ta kashe aure ta gusar da zaman lafiya a gidaje da dama, kayi taka tsantsa wajen kiyayewa.

Ka sani zaku iya gamo da jarrabawa kalala a cikin aurenku; na dukiya, rashin lafiya, yara, haihuwa, makota, iyaye, 'yan uwa, abokai, abun hawa, kasuwanci, karatu, aiki, tafiya da sauran su.

20. Ku rege Allah ya zama abun dogaro a cikin rayuwar ku dana auren ku, ka sani a duk lokacin da kuka bar


Allah acikin alamuran ku zai barku da wayo da wayewarku ne wajen warware matsalolin ku wadda ni da kai duk mun sa bin wayo da wayewa bata bullewa kowa.


21. Ka zama mai sirri da samun nagaba dashi wajen neman shawara, Karka taba zama cikin 'yan "hide my Id" 99% din su basa samun mafita face baki da suke jawoma kan su da lalacewar auren su.


Wanna kadan ne daga cikin abunda zan ya fadama kasancewar tsawon rubutu.


Ina mai muku fatan alkhairi da zaman lafiya a cikin auren ku.

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home