Ba zan iya samun kamarki ba a rayuwa ba – Mijin Lailah Othman
A yau ne lailah othman take murna zagayowar ranar haihuwar na shekara 38 a duniya shine mijinta ya aika mata sakon murna wanda ya dauki hankalin jama’a duba da abinda ya faru yan kwannan akan wani bidiyo da sadiya marshal ta cacake ta.
Ga sakon mijin nata.
Dan Majalisar tarayya Shugaban Kwamitin Sojojin ruwa Rt. Hon. Dr Yusuf Adamu Gagdi ya rubuta wasikar soyayya ga matarsa Layla Ali Uthman wannan na kunshe a cikin Sakon sa na Murnar zagayowar Haihuwa Yana Mai cewa A wannan rana taki ta musamman, ina da bakin magana don isar da kyakkyawar godiyata ga Allah SWT da ya halicci irin wannan halitta ta musamman, kuma mafi mahimmanci.
Ba zan iya samun wacce fi ki dacewa ta sanar da ni ƙima a rayuwata ba, Ina maki fatan rayuwa mafi kyau da za ta iya ci gaba a irin wannan bukin cika shekaru 38 na haihuwar ku.
Matata masoyiyata, ki ci gaba da kasancewa ke da na hadu da ita kuma na kamu da ita, yayin da nake ci gaba da addu’a cewa soyayyar da ta daure mu ta ci gaba da toho a cikin zukatanmu.
Barka da zagayowar ranar haihuwarki, Laylah Ali Othman Gagdi, Sarauniyar Al’ummata, da fatan Allah ya karo shekaru masu albarka cikin koshin lafiya.
A yau ne Laialh Othman Take cika shekaru 38 a duniya shine mijinta ta saki zafaffan kalaman soyayya akanta da ya dauki hankalin Mutane, duba da yadda bidiyon Caccakarta ya karaɗe shafukan sada zumunta
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home