Saturday, December 23, 2023

HOTUNA: “Labarin yadda matar aure Hafsat ta cakawa saurayinta Wuƙa har lahira a jihar Kano”

 






HOTUNA: “Labarin yadda matar aure Hafsat ta cakawa saurayinta Wuƙa har lahira a jihar Kano”


Tun farko matar mai suna Hafsat tana soyayya da Tasi'u ne ba tare da mijinta ya sani ba, shaƙuwar su har ta kai idan zata tafi aikin Umrah a ƙasa mai tsarki bata tafiya da mijinta sai da shi saurayin nata tare suke tafiya ko wani guri shi ke tuƙa ta, shi kuma mijin ba yadda ya iya saboda ta fishi kuɗi, kuma ana zargin ɗanɗan data haifawa mijin nata ba nashi neba saboda jama'a na maganar cewa yaron yana kama ta saurayin nata sosai, kwatsam sai Tasi'u ya fada mata cewa aure zai yi daga nan ta hau kishi tana son hana shi har saɓani ya soma shiga tsakanin su


Takaici ya dameta tayi yunƙurin kashe kanta sai saurayin nata ya hana ta daga nan ta caccaka masa Wuƙa wanda hakan yayi sanadiyar mutuwar sa yanzu haka Hafsat tare da mijinta da kuma malamin da aka kira yayi wa gawar Tasi'u wanka suna hannun ƴan sanda


Muna roƙon Allah ya raba mu da mummunar ƙaddara

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home