Monday, December 4, 2023

GARKUWA DA MUTANE: Kotu ta yanke wa Sarkin Fulani, Usman daurin rai da rai






Babban kotu dake Ilorin babban birnin jihar Kwara ta yanke wa wani basarake da wasu mutum biyu hukuncin ɗaurin rai da rai bayan an same su da laifin yin garkuwa da mutane.


Kotun ta tuhumi sarkin Fulani Usman Adamu, kanensa da wani Gidaddo Idris bisa zargin aikata laifin hada baki da yin garkuwa da mutane.


Alkalin kotun Adenike Akinpelu bayan ya yanke hukuncin ya ce abin tashin hankali ne yadda sarakunan gargajiya da aka dorawa nauyin kare rayuka da dukiyoyin jama’a ke cutar da mutane saboda son rai da son duniya.


Akinpelu ya kuma umarci mutanen da su biya wanda suka yi garkuwa da shi naira 600,000 diyyar muzguna masa da suka yi.


Shugaban fannin dake gurfanar da masu aikata laifi irin haka na jihar Idowu Ayoola ne ya shigar da kara kotu.


Ayoola ya ce Adamu da abokan sa sun yi garkuwa da wani Abubakar Ahmad a shekarar 2022.


Ya ce Adamu ya yi tsawon kwanaki 20 a hannun waɗanda suka kama shi sannan suka sake shi bayan ƴan uwan shi sun biya Naira miliyan daya kudin fansa.

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home