Abin Da Dahiru Bauchi Ya Ce Kan Sauya Sunan Kauyen Tudun Biri...
Shahararren malamin Musulunci kuma jagoran Darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya ce sauya sunan gari abu ne da ya shafi al’ummar garin, idan kuma mutanen Tudun Biri suka zabi sauya sunan garinsu zuwa Tudun Maulidi, ya fi.
Sheikh Dahiru Bauchi ya yi wannan kalami ne a ranar Asabar lokacin da aka tambaye shi cewa ko da gaske ne ya sauya wa garin suna zuwa Tudun Maulidi daga Tudun Biri.shafin jaridar liberty tvr na ruwaito a shafinsu.
Sai ya ce “Idan mutanen garin suna so sai su sauya wa garin nasu suna zuwa Tudun Maulidi, ya fi.
“Saboda shi biri halinsa barna ne, Maulidi kuwa tuna tarihi ne na rayuwar Manzon Allah Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wa Sallama.”
Sai malamin ya yi addu’ar samun rahama ga wadanda harin bom din da jirgin soja ya jefa a wurin Mauludi a garin ya shafa.
Ya kuma yi addu’ar samun lafiya ga wadanda suka samu raunuka a harin da kuma na samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.
Tun lokacin da al’amarin ya faru dai malamin mai shekaru kusan 100 a duniya ya roki Gwamnatin Tarayya da ta binciko musabbabin faruwar hakan, kuma ta biya diyyan ga wadanda suka rasa rayukansu da kuma wadanda suka sami raunuka.
Sai dai a ranar Juma’a ne wasu suka rika sanya bayanai a intanet cewa malamin ya sauya wa garin suna zuwa Tudun Maulidi daga Tudun Biri.
Hadiman shehin da wakilin Aminiya ya zanta da su suka batun sauya sunan gari lamari ne na mutanen garin da mahukunta.
Amma babu laifi idan aka ba da shawara, suka karaba kuma suka sauya, domin yin haka zai sa a rika tuna wannan waki’a da ta sami mutanen garin lokacin da suke bukin Maulidi.
0 Comments:
Post a Comment
Subscribe to Post Comments [Atom]
<< Home