Thursday, July 6, 2023

Abubuwa 5 da Suke Jawo Bala’i Acikin Al’umma












Abubuwa 5 da Suke janyo Bala’i Acikin Al’umma

Hadisi Ya Tabbata daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya ƙara masa yarda)

Yace Watarana muna zaune sai ga Manzon Allah (S.A.W) yazo wucewa, Yace ” ya ku taron muhajirai! Akwai wasu abubuwa guda 5 idan al’umma suka Jarabtu dasu!

Ina Roƙon Allah kada ku riske wannan Lokaci.

1 Duk Al’ummar da suka bayyana Alfasha! Tabbas zasu samu kansu cikin Annoba da yaduwar sabbin cututtukan da ba’a taɓa ganin su ba!

2 Duk Al’ummar da suke tauye modu da sikeli! Tabbas zasu samu kansu cikin yanayi na fari (rashin ruwan sama), Tsadar Rayuwa da cutarwa daga azzaluman Shuwagabanni.

3 Duk Al’ummar da suka hana zakkar dukiyoyinsu! Tabbas Allah zai hanasu ruwan sama! Idan kaga Ruwa, an yine kawai saboda yara da dabbobi da suke rayuwa a cikinsu.

4 Duk Al’ummar da suka saɓa alkawarin Allah da Manzon sa! Tabbas Allah zai ƙasƙantar dasu a gaban abokan gabansu.

5 Duk Al’ummar da Shuwagabaninsu basu hukunci da Littafin Allah, kuma suke chanza Abinda Allah ya sauƙar! Tabbas Allah zai sanya gaba, yaƙi da ganin Aibin Junansu a tsakaninsu.

Ibn Majah ne ya Rawaito Wannan Hadisin.

Dan Girman Allah acikin Waɗannan Abubuwa 5 wanne ne ba’a aikatawa a Nigeria? A hakan kuma muke jiran ganin dai dai

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home