Sunday, May 21, 2023

Kalli Bidiyon Wata Budurwa Data Kusan Mutuwa Sanadiyyar Shaye-Shaye Kalli Bidiyon Anan

Kalli Bidiyon Wata Budurwa Data Kusan Mutuwa Sanadiyyar Shaye-Shaye Kalli Bidiyon Anan.......















Kalli Bidiyon Wata Budurwa Data Kusan Mutuwa Sanadiyyar Shaye-Shaye Kalli Bidiyon Anan

Cigaba da bayani kan Illolin shaye shaye…



Ita dai wannan ɗabi’a ta zama ruwan dare a cikin al’umma, matasa samari, yanzu abin tashin hankalin shine harda yan mata a harkar shaye shaye, kuma tabbas wannan matsala tanada matukar illa ga masu yinta da al’umma gaba ɗaya.



Illar shaye shaye ga lafiya.

~ Tana haifar da lalacewar huhu wato “lungs” ga masu ta’ammali da kayan hayaki.

~Tana haifar da magani yadena yiwa mutum aiki a lokacin da ake bukatar hakan, saboda jikinsa, ya riga ya raina adadin yadda zaiwa magani.



~ Kuma yakan taɓa kwakwalwa, wasu har haukachewa sukeyi gaba ɗaya.



A ɓangaren mu’amala.

Dan shaye shaye yana zama kamar mahaukaci acikin al’umma, saboda haka zai zamo abin kyama, Kuma shaye shaye nasa mutum ya zama mai dogon hannu wato “ɓarawo” tun daga gida har ta kai ga jama’ar unguwa, kuma sukan tsargu da kansu Dan haka ake saurin samun matsala dasu, Sai uwa uba, rashin girman na gaba, saboda Shaye shaye nasa mutum yaji dai dai yake da kowa.

ILLAR SHAYE-SHAYE A RAYUWA.




Ya kamata matasan arewa su nisanci shaye-shayen miyagun kwayoyi domin yin rayuwa Mai inganci.



Daga. YGM.



Kiran Rundunar matasan Mani ta Gabas ga iyaye da su tashi tsaye wurin kula da tarbiyar ‘ya’yansu matasa maza da mata.



Shaye-shaye ya zama ruwan dare a tsakanin al’umma musamman ma matasa maza harda mata, masu aure da wadanda basu da shi.



Shaye-shaye na nufin duk wani yanayi da mutum zai sa kanshi don sauya yanayin tunaninsa ko nazarinshi ta yadda ba zai iya auna yakamata ko akasin haka ba.



Shaye-shaye na zuwa ne a duk lokacin da mutum ya afka cikin Shan kwayoyi, sabanin yadda lilkita ya kayyade a sha, Shan giya ko tabar wiwi da dai sauran nau’ikan sinadarai masu bugar da mutum ko su Kai ga maye, da aikata wasu abubuwa na rashin hankali.



Wasu daga cikindalilan dake angiza wasu shiga shaye-shayen sun hada da jahilci, matsalolin rayuwa, al’ada, hulda da abokan banza, aikin karfi da kuma samun kyayoyin cikin sauki.



Shaye-shaye na zubar da mutunci, janyo talauci da jahilci, ciwon huhu, ciwon hauka, ciwon hanta, ciwon kansa, ciwon suga da kuma ciwon sanyin Kashi, sannan yana kawo lalaci da rashin kuzari, yadda Mai shaye-shaye ba zai iya katabus ba, tare da lalacewar mazakunta da dai sauransu.



Duk da irin kokarinda Gwamnati da hukumomi a matakai daban-daban ke gudanarwa wajen hana shaye-shaye, safarar kwayoyi da sauran kayan maye. Har ila yau ya zama dole iyaye su tashi tsaye don kula da tarbiyar’ya’yansu.

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home