Wednesday, May 17, 2023

Hadin Namijin Goro Da Gyada Domin Magance Saurin Inzali Da Karin Ruwan Maniyi Da Dadewa Yayin Saduwa Da Iyali

Hadin Namijin Goro Da Gyada Domin Magance Saurin Inzali Da Karin Ruwan Maniyi Da Dadewa Yayin Saduwa Da Iyali....















Ba shakka lallai wannan fa’ida ta kuke karantawa fa’ida ce wacce Al’umma da dama sukai amfani da ita kuma tayi musu tasiri wajen maganin shaanin daya shafi jima’i.



Hakan yasa naga ya dace ya rubuta ta ga sauran Al’umma domin suma su samu su amfana da ita wajen magance abinsa yake damun su bangaren zamantakewar aure.


Wannan fa’ida tana kara Sha’awa sannan tana kara ruwan maniyi tana maganin saurin Inzali tana karawa namiji shaawa da kuzari da nishadi da jin dadi a lokacin saduwa da iyali.

Abubuwan da zaka samo domin hadawa sune abubuwa kamar haka:-

Na farko shine zaka samo Namiji goro kamar guda goma 10 zaka shanya su, su bushe a inuwa amma ka fara yayyanka su kanana domin su bushe da wuri,idan ya bushe zaa dake shi yayi laushi.

Sannan abu na biyu zaka samo Gyada Soyayyiya (Amarau) zaa gyara ta ka hafe da wannan Garin Namijin goron ka dake sosai,gyadar zaa samo kamar rabin gwangwani ne.

Sai a rika diban karamin chokali (Teaspoon) ana zubawa a mafara ta ruwa ana sha,ko a sha a yogurt ko nono ko kunu ko koko sau 2 a rana tsawon sati 2 insha Allah zaa dace.


Ga Wani Hadin Kuma Na Fireless Da Madara Peak

Aslm Idan ka san baka da aure kar ma ka tsaya bata lokaci wajen karanta wannan fa’idah mai matukar amfani ga ma’aurata

Ga wani Mujarrab ku gwada yana da matukar tasiri da armashi a babin raya sunnah ta Ma’aiki (SAW)

Kawai ku je shago, ku sayo Fearless da Peak Milk, sai a sayo ayaba ta naira 100 kacal ya isa

Bude murfin Fearless din, a juye madaran Peak Milk a ciki, a jijjiga sosai, sai ka shanye abinka tas kar ba bawa uwargida, bayan kaci ayaba kamar guda 4 ko 2 ma ya wadatar

Ma’aurata zakuyi wannan hadin ne bayan mintuna 30 kafin a kai ga raya Sunnar Manzon Tsira Annabi Muhammad (SAW), maza kadai zasuyi banda mata

Wannan Hadin a zamanke ne ba tare da kasha wata wahalar neman yayan itatuwa ba

sai dai ina muku fatan alheri tuzurai maza da mata, Allah Ya aurar daku ku dandana dadi da albarkan da muke sha a gidan aure.

Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan maganin zamu so karben ra’ayoyinku a sahen mu na tsokaci.

0 Comments:

Post a Comment

Subscribe to Post Comments [Atom]

<< Home